Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya bayyana wa wakilan jam’iyyar PDP a garin Abeokuta jihar Ogun cewa shi fa ba da wasa yake yi ba a wannan takara da ya fito.
Bukola ya ce ya shirya kayan yakin sa kaf domin wancakalar da Buhari a zaben 2019.
” In rokon ku da ku mara mini baya sannan ku zabe ni a zaben fidda gwani da za ayi ranar 5 da 6 ga watan Oktoba in zama dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP.
” Lokaci ne yanzu yayi da ake bukatar mutum mai karfi a jika ya shugabanci kasar nan kamar yadda yake a wasu kasashen duniya. Na yi abin azo a gani a tsawon shekaru na a harkar siyasar Najeriya wadda a dalilin haka nake ganin nafi kowa cancanta domin cira tutar PDP a zabe mai zuwa.
Shi ko babban kanzagin Saraki sanata Dino Melaye, bayan wakoki da rera kira yayi ga mutanen Najeriya da su tabbata sun wancakalar da Buhari a zabe mai zuwa.
” Kamata ya yi duk mu hadu mu maida Buhari garin Daura can ya koma gida ya huta bayan ya kammala wa’adin mulkin sa na farko.” Inji Dino