Hukumar EFCC ta rubuta wa Hukumar Kwastan ta Najeriya wasikar cewa su sa-ido sosai a kan Gwamnan Ekiti, Ayo Fayose domin hana shi ficewa daga kasar nan.
Hukumar ta rubuta takardar ne a ranar 12 Ga Agusta, ta na mai jan kunnen kwastan da Ayo Fayose barazana ne ga zirga-zirga, kuma zai iya ficewa daga kasar nan, ko ta sama, ko ta ruwa ko ma ta kan iyakoki ta kasa.
Shi dai Fayose zai kammala shekarun sa hudu na gwamna a karo na biyu, a ranar 16 Ga Oktoba.
Magu ya shaida wa hukumar kwastan a Abuja cewa Fayose ya na fuskantar laifukan da suka hada da hadin-baki, makarkashiya, kin bin tsarin aikin ofis, rashawa da cin hanci, sata da kuma karkatar da kudade.
Daga nan ita kuma hukumar kwastan sai ta rubuta takarda, inda ta nemi shiyyoyin ta na fadin kasar nan da su tabbatar da cewa sun tare duk wata hanya da Fayose zai iya bi ya gudu daga kasar nan.
An rubuta wannan wasika ce kuma aka raba wa masu kula da shiyyoyi da jihohi a ranar 14 Ga Disamba.
Wadannan wasiku biyu sun shigo hannun PREMIUM TIMES a ranar Lahadi, kwana daya tal bayan an kyale Kemi Adeosun ta gudu daga Najeriya.
Kemi dai za ta iya fuskantar daurin shekaru 14 a gidan kurkuku saboda laifinnkaryar mallakar takardar NYSC ta bogi.
Kemi ta yi murabus a ranar 14 Ga Satumba, kuma ‘yan kasar Birtaniya ce, sannan kuma gwamnatin Najeriya ba ta nuna cewa za ta gurfanar da ita a gaban kotu ba.
Kokarin yi wa Fayose kofar rago ya zo ne bayan ya rubuta wa EFCC wasika cewa zai kai kan sa domin a bincike shi, kwana daya bayan ya sauka daga mukamin gwamnan Ekiti.
Kwana daya bayan da EFCC ta bayyana cewa a hana Fayose ficewa daga kasar nan, ya shiga kafafen yada labarai ya gwasale hukumar cewa abin na ta har ma da sokonci, domin shi ne da kan sa ya rubuta takarda cewa zai kai kan sa.
Ya kuma soki gwamnatin Buhari da bin ‘yan adawa ta na yi musu bi-ta-da-kulli, a gefe daya kuma ta kyale na cikin gwamnati.