Tawagar gwamnan Zamfara ta sha ruwan duwatsu

0

Tawagar motocin Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari, ta sha ruwan duwatsu ranar Lahadi, daga hasalallun ‘ya’yan jam’iyyar APC, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) ya ruwaito.

Yari, wanda jihar sa Zamfara ke fama da hare-haren ‘yan fashi da masu garkuwa da jama’a, shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya.

NAN ta ruwaito cewa an tare jerin gwanon motocin Gwamnan a daidai shataletalen Lalan a cikin Gusau, a lokacin da ya ke kan hanyar tafiya Kaduna.

Bakwai daga cikin ‘yan takarar gwamnan a karkashin APC, ciki har da mataimakin sa Ibrahim Wakkala sun shirya taron gangamin karbar su, inda ‘yan jam’iyyar da yawan gaske suka halarci taron.

A yayin da magoya baya da kuma ‘yan takara ke shigowa cikin gari, sun yi kicibis da jerin gwanon motocin gwamnan, daga nan suka hau su da jifa, har aka farfasa masu gilasan motoci.

Sai dai kuma gaggawar isar ‘yan sandan mobile da kuma jami’an tsaron gwamnan wadanda suka rika yin harbi a sama, ya tarwatsa taron hasalallun.

NAN ta ruwaito cewa a yanzu dai kalau ake zaune a cikin garin Gusau, tun bayan kwantar da rikicin.

Ba a dai san takamaimen dalilin kai wa gwamnan hari ba, sai dai kuma ba zai rasa nasaba ba zaben dan takarar da zai maye gurbin Gwamna Yari ba, bayan ya gama wa’adin mulkin sa cikin Mayu, 2019.

A cikin wata samarwa da Yari ya fitar a jiya Lahadi, ta hannun Jami’in Yada Labaran sa, Ibrahim Dosara, ya ce aikin ‘yan adawa ne, kuma ya ja hankalin magoya bayan sa cewa kada su sake su nemi daukar fansa.

Ya yi kiran a zauna lafiya.

Can a wurin gangamin ‘yan neman takarar gwamna su bakwai kuwa, sun yi kiran cewa a yi zaben fidda-gwani, ba su yarda da zabin da gwamna ya yi na wanda zai maye gurbin sa ba.

Cikin wadanda suka yi jawabi a wurin gangamin har da tsohon gwamnan jihar, Mamuda Shinkafi, kuma ya na cikin ‘yan takara.

Dukkan ‘yan takarar su bakwai ba wanda bai yi jawabi ba.

Baya ga Shinkafi, sauran ‘yan neman takarar a karkashin APC sun hada da: Ibrahim Wakkala, Aminu Jaji, Sagir Hamidu, Mansur Ali, Abu Magaji da kuma Dauda Dare.

Share.

game da Author