Gwamna Ganduje ya zabi mataimaki

0

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya zabi kwamishinan gona, Nasiru Gawuna a matsayin mataimakin sa.

Ganduje ya mika sunan sa a Majalisar Dokokin Jihar Kano, domin tantancewa inda Gawuna zai maye gurbin Hafiz Abubakar, wanda ya yi murabus cikin watan da ya gabata.

Da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kabiru Rurum ke karanta takardar Gwamnan, a yau Litinin, y ace wasikar ta yi daidai da abin da dokar kasa ta sashe na 191 (3) (C) ta 1999 ta tanadar a yi.

A cikin wasikar, Gwamna Ganduje ya yi fatan cewa majalisar za ta amince da shi, kuma ya tabbatar ya yi zabin alheri, bai yi zaben-tumun-dare ba.

Majalisar ta gayyaci Gawuna ya bayyana a gaban ta gobe Talata, domin tantance shi.

Gawuna ya taba yin shugabancin Karamar Hukumar Nassarawa a zamanin mulkin Ibrahim Shekarau a zangon san a farko, sannan kuma a zangon Gwamna Rabi’u Kwankwaso ya yi Kwamishinan Ayyukan Noma da Ruwan Sha.

Lokacin da Ganduje ya zama gwamna a 2015, sai ya sake nada shi kwamishinan ruwa, mukamin da Kwamkwaso ya fara nada shi a 2014.

Share.

game da Author