Lokacin ‘yan kin Arewa ta Tsakiya ya yi su yi shugabancin Najeriya – Saraki

0

Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ya bayyana cewa lokaci yayi da dan yankin Arewa ta Tsakiya ya zamo shugaban kasar Najeriya.

Saraki ya bayyana haka ne a garin Jos a wajen taron wakilan jam’iyyar PDP na jihar.

” Mu ‘yan jihohin Kwara, Filato, Benuwai, Kogi da Nasarawa mun bauta wa kasar nan matuka sannan duk hadin kan mu yanzu mun sami rarrabuwa matuka. Dole mu dawo mu dinke tamau domin samun wannan dama.

” Muna neman shugaban kasan da zai ja kowa a jika, Wanada kowa na shi ne, wanda duk ‘yan Najeriya na sa ne kuma ya dauki kowa daya.

” Lokacin mu yayi yanzu, dole mu canja fasalin mulki a kasar nan mu karkato da akalar zuwa wannan yanki . Dole ‘yan Najeriya su hada karfi da karfe domin a ceto Najeriya daga halin da ta shiga.

Saraki ya kara da cewa shi shugaba ne mai adalci, kishi da sanin ya kamata, cewa kowa ya ga yadda ya ke shugabantar majalisar dattawa ba tare da nuna bambanci ba.

Share.

game da Author