Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa kurari da barazanar da jam’iyyar APC ke yi masa ba za su sa ya sauka daga shugabancin majalisa ba.
Saraki ya bayyana cewa sai dai a hakura har wa’adin shugabancin sa ya cika sannan ya sauka.
Saraki ya kara da cewa jam’iyyar APC ba ta iya cire shi daga shugabanci domin ba ta da yawan ‘yan majalisar da doka ta amince sai sun kai wannan adadin ne za su iya tsige shi.
Haka dai jaridar Thisday ta ruwaito.
Saraki ya yi wannan jawabi ne a yayin da ya kai ziyarar neman goyon bayan tsayawa takara a jihar Neja a wurin tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangid da kuma ofishin PDP na jihar.
Wannan ce ziyarar da Saraki ya kai wa Babangida ta biyu a cikin wata daya.
Kafin wannan ziyara kuma sai da ya kai wa Olusegun Obasanjo ziyara, a Otta, jihar Ogun.
Duk da Saraki bai bayyana dalilin ziyarar ta sa ba, amma bai ba ta rasa nasaba da batun neman goyon bayan tsayawa shugabancin kasar nan a zaben 2019, a karkashin jam’iyyar PDP.
Kusan kullum dai sai shugaban jam’iyyar APC, Adams Oshimhole ya yi kurari da zare idanu cewa ko dai Saraki ya sauka, ko kuma a tsige shi.
Shugaban Majalisar ya shaida wa magoya bayan PDP a hedikwatar ta da ke jihar Neja cewa PDP ce ke da rinjaye a majalisar dattawa, don haka babu wani kurari ko bude-idanu da APC za ta yi masa har ta tirsasa shi ya sauka.
Saraki ya ce majalisa ba za ta dawo da zama ba sai wa’adin hutun da ta tafi ya cika. Domin a bisa ka’idojin doka ta tafi hutun.
Don haka ya ce maganar da APC ke yi wai a dawo da zama a tsige shi, ya ce tatsuniya ce kawai, domin ba za a dawo din ba, sai lokaci ya yi.
Idan ma lokacin dawowar ya yi, Saraki ya ce ba ya tsiguwa sai ya kammala shekarun sa hudu a kan shugabancin majalisar dattawa da ya ke yi a kai.