A yammacin Lahadi ne dakarun sojin Najeriya suka yi arangama da wasu ‘yan Boko Haram da suka yi musu kwantar bauna a hanyar Maiduguri zuwa Bama.
Rundunar sojin kasa ta sanar da haka ne a shafinta na tiwita in da ta shaida cewa ta samu galaba a kan wadannan yan ta’addan.
” Bayan fatattakan su da muka yi mun kwato bindigogi biyu da harsasai masu yawa.