Bangaren jam’iyyar APC a jihar Adamawa dake adawa da shirin zaben fidda dan takara ta hanyar amfani da deliget da jam’iyyar a Jihar ta amince da ta jadda rashin amincewar ta a wani taro da ta yi a Abuja.
Mambobin wannan bangare na APC sun bayyana cewa wannan shiri bai dace da jihar ba kuma suna adawa da ita.
Wadanda suka halarci wannan zama sun hada da tsohon shugaban hukumar EFCC, Nuhu Ribadu, Babachir Lawal, Ahmed Mo’Allayidi, Abubakar Girei, Bello Tukur, Marcus Gundiri, Sadiq Muhammed (Walin Ganye) da Mahmoud Halilu.
Bangaren sun yi kira ga uwar jam’iyya da ta tilasta wa jam’iyyar a jiha ta yi amfani da shirin ‘Direct’ wato amfani da duk ya’yan jam’iyyar maimakon deliget.
” Mu duka a nan, ‘yan takara da jiga-jigan jam’iyya da wasu deliget ba ma tare da wannan hukunci da jam’iyyar ta yanke a jihar kuma muna kira da kakkausar murya da ta janye haka a dawo ayi amfani da abin da ya fi dacewa.
Sannan muna so mu sanar wa uwar jam’iyya cewa jihar Adamawa a shirye take ta yi zaben fidda dan takara ta hanyar ” Kato a bayan Kato wato ‘Direct’.
Discussion about this post