Gwamnati za ta bunkasa cibiyoyin kiwon lafiya don fara kula da masu manyan ciwo

0

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa gwamnati na kokarin ganin ta inganta cibiyoyin kiwon lafiya don ganin suma sun fara kula da mutane daka fama da manyan cuwuka, kamar su Hawan Jini, Ciwon Siga da sauran su.

Adewole ya bayyana haka ne a taron masana harkar kiwon lafiya da aka yi a garin Abuja.

” Za a yi haka ne domin a rage yawan cinkoso da ake samu a manyan asibitocin kasar nan.

” Bincike ya nuna cewa mutanen da suka rasa rayukan su a dalilin kamuwa da cutar hawan jini a kasar nan sun kai 10,864 sannan wadanda suka mutu a sanadiyyar cutar siga sun kai 30,922.

A karshe jami’ar asibitin koyarwa na jami’ar Abuja Felicia Anuah ta yi kira ga mutane da su riga sanin matsayin kiwon lafiyar su a asibiti domin kamuwa da irin wadannan cututtuka basu nuna alamu da wuri.

Share.

game da Author