Sanata Kabiru Marafa na majalisar dattawa ya ce idan har da gaske gwamnan jihar Zamfara Abdul-Aziz Yari ya ke yi cewa da yayi wai zai yi murabus a dalilin rashin tsaro da ake fama da shi a jihar.
Marafa ya bayyana haka ne da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa jim kadan bayan ya gana da shugaban kasa.
Ya ce babban dalilin ganawar sa da shugaba Buhari shine don ya fada masa gaskiyar abin da ke faruwa a jihar Zamfara game da tsaro.
” Bai yiwuwa a ce a na ta kashe makudan kudade kan tsaro ba amma jiya-i-yau, shine ya sa na garzaya fadar shugaban kasa domin in sanar masa da gaskiyar abin da ke faruwa a jihar Zamfara da irin tsananin wahalar da mutane ke sha a jihar a dalilin rashin iya mulkin gwamnati mai ci.