Kotun dake Grade 1 a Abuja ta yanke wa Amina Ishaq mai shekaru 22, Praise Bassey mai shekaru 29 da Mariam Soliu mai shekaru 23 da suke zama a unguwar Mpape hukuncin zama a kurkuku na tsawon kwanaki 45 sanadiyyar ba hammata iska da suka yi a tsakanin su.
Lauyar da ta shigar da karar Ifeoma Ukagha ta bayyana a kotun cewa sai da wadannan mata suka gama damben su sannnan suka kwashi kan su da kan su suka mika kan su ga ofishin ‘yan sanda.
” Matan sun ji wa juna munanan rauni.”
Alkalin kotun Inuwa Maiwada ya yanke wa matan hukuncin dairin kwanaki 45 a gidan yari ko kuma kowannen su ta biya taran Naira 3,000.
Maiwada yace ya yanke wa wadannan mata wannan hukuncin ne saboda sauran mutane su dauki darasi da sannan su guje wa aikata irin haka.
Discussion about this post