Mahara sun far wa wani gidan kallon kwallo dake Badarawa a karamar hukumar Shinkafi jihar Zamfara.
Maharan dauke da bindigogi sun kashe mutane 11 sannan wasu 21 sun tsira da raunuka a jikin su a daidai suna kallon kwallon a gidan.
Kakakin gwamnan jihar Ibrahim Dosara ya bayyana haka wa PREMIUM TIMES inda ya kara da cewa maharan sun far wa wannan gidan kallo ne a daren Laraba.
” A yanzu dai mutanen da suka sami rauni na samun kula a babban asibitin Shinkafi sannan jami’an tsaro sun fara gudanar da bincike domin gano wadanda suka aikata wannan mummunar aiki.
Sai dai kuma a jawabin da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammed Shehu yayi, ya ce mutane shida ne suka rasa rayukan su a harin sannan 10 ne kawai suka sami rauni.
Shehu yace sun gaggauta zuwa wannan wurin ne bayan sanar dasu abin da ya faru a kauyen Badarawa.
Za mu bincika dazukan dake kewaye da kauyen Badarawa domin ta nan ne maharan suka gudu sannan za kuma mu kafa shingaye hanyoyin da ake shiga dajin.