Dalilan da ya sa na fito takarar sanata a jihar Filato – Pauline Tallen

0

Tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar Filato Pauline Tallen ta bayyana wasu dalilan da ya sa ta fito takarar kujerar sanata na Jos ta kudu.

Idan ba a manta ba Pauline ta yi ministan kimiyar da fasaha a mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo sannan ta kuma yi mataimakiyyar gwamnan jihar Filato.

A yanzu haka Jeremiah Useni ne ke wakiltan shiyar Jos ta kudu wanda shi kuma ke haran kujeran gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar PDP.

Sai dai ita kuma Pauline za ta shiga kokuwar wannan kujerar ne a inuwar jam’iyyar APC da dan takarar Jam’iyyar PDP Ignatius Longjan wanda gwamnan jihar Solomon Lalong ke marawa baya.

” Sanin kowa ne cewa ni mace ce da bata nuna kabilanci, bambamci ko wariya.

Ta kuma ce ta amince ta fito takara ne saboda karancin yawan matan da ake da su a harkokin gwamnatin kasar nan.

” Bayanai sun nuna cewa idan har kasa na bukatan ci gaba kamata ya yi a jawo mata a harkokin gwamnati.

Ta ce a dalilin haka ne take kira ga gwamnatin Najeriya da ta dauki darasi daga kasashen Senegal, Kenya, Gambia da Ghana game da yadda suka bar kashi 50 zuwa 60 bisa 100 domin mata su sami damar taka rawa a harkokin gwamnatin kasashen su.

Share.

game da Author