Rantsuwa ya kubutar da auren Hajara da Albashir a Kaduna

0

Hajara Ibrahim matar Albashir Ibrahim ta kai karan mijinta a kotun shari’ar dake Magajin Gari a Kaduna cewan mijinta Ibrahim ya sake ta sannan ya hana ta tafiya gidan su.

Hajara ta ce a dalilin haka ne take bukatan kotu ta sa baki a maganar domin samun matsaya.

Ibarahim ya karyata duk abin da Hajara ta fada a kotu cewa ba shi da masaniyar cewa ya saki matar sa.

Bayan ya fadi haka ne alkain kotun Dahiru Lawal ya bukaci Ibrahim da ya rantse bisa kan abin da ya fada.

Nan da nan kuwa Ibrahim ya daga muryar sa ya ce ” Na rantse da mahallaci na ni Albashir Ibrahim ban saki matata ba Hajara sannan idan har na sake ta ko kuma na fadi wa wani na sake ta kuma nayi karya a kai Allah ya sauko da la’antar sa a kai na.”

Da jin haka sai alkali Lawal ya hori Hajara da ta koma gidan mijinta ta ci gaba da zaman auren ta ganin cewa Hajara ta kasa gabatar wa kotu shaidar sakin da Ibrahim ya yi mata.

Bayanai sun nun ace bisa ga addinin musulunci idan irin wannan gardadama na saki ya shiga tsakanin miji ta mata kuma ita matar bata da shaidar sakin da za ta gabatar akan sa mijin yayi rantsuwa ne.

Share.

game da Author