A ranar Laraba da rana ne wani matashi mai shekaru 28 Nurudeen Iliyasu ya dare kololuwar tsanin da ake kafa na’urar wayar tafi da gidan ka don nuna fushin sa ga durkushewar tattalin arzikin Nageriya.
Iliyasu ya dare wannan tsani ne a garin Abuja dauke da wasu rubuce rubucen da ke nuna bacin ran sa ga yadda al’amura ke gudana a kasar nan.
Iliyasu ya bayyana cewa zai zauna a kan wannan tsani na kwanaki bakwai sannan ba zai damu ba koda zai rasa ran sa ne.
” Koma bayan tattalin arzikin da muke fama da shi a kasar nan ya hana mutane sakat. An wayi gari mutane da dama basu iya ci abinci saboda talauci, rashin aikin yi, rashin samun ababen more rayuwa da sauran su.
” Burina za ta cika idan har na mutu a nan idan dai hakan zai kawo canji a kasar nan.
Bayan haka likitoci sun bayyana cewa Iliyasu zai iya rayuwa na tsawon wasu ‘yan kwanaki idan yana shan ruwa kadai.
A karshe mai gadin wannan tsani Ayuba Luka ya bayyana cewa a wannan rana Iliyasu ya nemi izinin sa domin ya dare wannan tsani ammm ya ki amincewa.
Discussion about this post