Matan aure mai sun Deborah Olusola ta maka mijinta mai suna Sunday Olusola a kotun Idi-Ogungun dake Ibadan jihar Oyo in da ta roki kotu da ta raba auren su.
Deborah ta na zargin mijin nata ne da laifin shirga mata karya sannan da aikata zina, da kuma yin wasu munanan ayyuka a matsayin sa na limamin coci.
” Na sha da kyar a shekara daya da watanni shida da na yi a gidan Sunday a matsayin matar sa domin bayan auren mu Sunday da sauran ‘yan uwan sa suka juya mini baya.
” Sunday ya fara wulakanta ni bayan na sami ciki sannan muguntar bai tsaya a kaina ba domin ya hada har da mahaifiya ta.
Deborah ta kuma bayyana a kotun cewa akwai ranar da ta kama Sunday a gado turmi da tabarya da kanwar sa.
Da ya tabbata na kama su sai ya yi mini barazanar ci gaba da muzguna mata idan har ta fadi wa wani abin da ta gani.
Ta roki kotu da ta raba auran su a bisa wadannan dalilai.
Bayan sauraran wadannan zarge-zarge da Deborah ta bayyana a Kotu, Sunday ya karyata duk abin da tace amma kuma ya roki kotu da ta raba auren shima ko ya huta.
Alkalin Kotun Mukaila Balogun ya raba auren sannan ya ce Deborah ta ci gaba da rike dan da suka haifa, shi kuma Sunday ya rika biyan Naira 3,500 duk wata kudin shayarwa.