Sharibu Nathan mahaifin Leah Sharibu wace Boko Haram suka sace tare da wasu matan makarantar Dapchi jihar Yobe ya bayyana cewa barayi sun shiga gidan sa sun sace masa kayan abinci da janareta.
Nathan yace barayin sun aikata wannan ta’asa ne ranar Litini sannan a unguwar da suke zama gidan su ne kawai suka shiga.
” Tabas an sace mana kayan abinci da janareta amma rashin wannan kaya bai kai radadin rashin Leah da muke ji ba.
” Saboda haka na ke cewa wannan duk ba komai bane.”
Bayanai sun nuna cewa barayi sun shiga gidan iyalin Nathan a lokacin da suka tabbatar babu kowa a gidan.
Sannan mutane sun sami labarin abin dake faruwa ne a lokacin da mahaifiyar Leah ta gane cewa barayi sun shiga gidan su.
A yanzu dai kwanakin Leah 207 a hannun ‘yan Boko Haram sannan a watan Agusta Boko Haram ta aiko da hoto da muryar Leah inda take kira ga gwamnatin Najeriya ta kawo mata dauki don ta dawo ga iyayen ta.
Gwamnati dai har yanzu bata ce komai ba game da wannan batu.