Ban yi na’am da hujjojin Shekarau na komawa APC ba, Ina nan a PDP – Sagir Takai

0

Babban na hannun daman tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, Sagir Takai ya bayyana cewa dalilan da mai gidan sa, wato Shekarau ya bada cewa sune suka sa ya koma jam’iyyar APC bai gamsar da shi ba da a haka yasa ya yaki bin sa.

Duk wanda ya san siyasar Shekarau toh ya ko san Sagir Takai domin shine ya zamo masa shafaffe da mai tun a 2011 da ya nemi ya gaje sa bayan ya kammala wa’adin sa na gwamna a jihar Kano. Haka kuma a 2015 ma shi dinne dai ya sake mara wa baya domin zama gwamnan jihar Kano amma duk suna shan kayi. Wancan karon a hannun PDP, wannan karon kuma a hannun APC.

Kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito, Takai ya yanke shawarar zama a PDP ne saboda dalilan da Shekarau ya bayar na fita daga jam’iyyar ba su gamsar da shi ba.

Ya ce mafi yawan mutanen da ya tuntuba kafin ya yanke wannan hukunci ta sauya shekar sun kwabe sa da ya hakura a inda yake ya ci gaba da zama a PDP din sa.

Amma Shekarau bai amince da wadannan shawarwari ba ya koma APC.

Takai ya ce alakar sa da Shekarau bai canza ba sai dai a siyasance yanzu ba su tare.

Tuni har takai ya kai ziyarar ga shugabannin jam’iyyar PDP a jihar wadda duk suna inuwar Kwankwaso ne yanzu.

Share.

game da Author