Sheikh Babantine ya rasu

0

Allah ya yi wa limamin masallacin rukunin gidajen Kamfanin mai ta Kasa NNPC dake Kaduna Sheikh Babantine rasuwa.

Yusuf Arrigassiyu ne ya tabbatar wa kamfanin dilancin labaran Najeriya haka.

Babantine ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Ahmadu Bello dake Zariya bayan yayi fama da rashin lafiya.

Tuni dai an yi jana’izar marigayi Babantine a makabartar Dambo dake Zariya.

Ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya 21.

Allah yaji kansa

Share.

game da Author