Dama ina kwana da yadda zan sayi fom din takara, sai gashi Allah ya yi mini gyadar dogo – El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyan cewa dama ya na kwana, yana tashi da tunanin yadda zai sami kudin da zai sayi fom din takarar ta zarce sai gashi Allah yayi masa gyadar dogo kungiyoyi sun siya masa.

Kudin fom din takara gwamna dai naira miliyan 22.5, kamar yadda jam’iyyar APC ta sanar.

Kungiyar Dillalan Man Fetur, IPMAN, Kungiyar Direbobin Tankunan Mai, PTD, Kungiyar Direbobin Motocin Haya, NARTO, Kungiyar ‘Yan kasuwan Sheikh Mahmood Gumi dake Kaduna da Kungiyar Katsinawa da Daurawa mazauna Kaduna ne suka yi karo-karo suka siya wa gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai fom din takarar ta zarce.

Jagoran gamayyar kungiyoyin Abbas Likoro ya bayyana cewa sun yi wa gwamna El-Rufai goma ta Alheri ne ganin yadda ya jajirce wajen yin aiki tukuru a jihar Kaduna.

” Dukkan mu mun gamsu da irin ayyukan ci gaba da gwamna El-Rufai ya ke yi a jihar Kaduna.

Mambobin kungiyoyin sun ya tattaki na musamman zuwa fadar gwamnati domin mika wa gwamna El-Rufai fom din.

A fadar gwamnati El-Rufai ya gode musu matuka inda ya ce dama can da tunanin inda zai sami kudin siyan fom din yake kwana ya da ita yaketashi.

” Tun da jam’iyya ta sanar da kudin fom din na fada cikin damuwa domin kuwa bani da irin wadanna kudi a asusun ajiya na banki.

” Shi kan sa shugaban kasa Muhammadu Buhari da yaji kudin sai da ya koka ya ce ba ya da wannan kudi. Bayan mun tafi kasar Chana sai mu ka yanke shawarar zamu yi karo-karo na naira Miliyan bibbiyu daga kowani gwamna domin siya masa fom din.

” Kwatsam sai muka ji wai wata kungiya ta siya masa fom din. Da na gaya masa sai ya tambayeni cewa ni kuma wa zai siya min.

El-Rufai ya gode wa wadannan kungiyoyi da suka yi masa wannan namijin kokari sannan suka fitar da shi kunya tun da bashi da kudin siyan fom din dama.

Ya shaida musu cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da yi wa mutane ayyukan ci gaba kamar yadda ta yi alkawari.

Share.

game da Author