ANA WATA GA WATA: Yari zai yi kokuwar Kujerar sanata da Yerima

0

A yau Litinin ne gwamnan jihar Zamfara AbdulAziz Yari ya bayyana ra’ayin sa na tsayawa takarar sanata a jihar Zamfara.

Wannan kujera dai da Yari zai nema ita ce tsohon gwamna kuma wanda ake wa ganin shine ubangidan sa, Ahmed Yerima ya ke kai a yanzu.

Yari ya ce dama can a harkar majalisa ya fi gogewa sannan daga nan ne ya samu gogewar sa ta farko a harkar siyasa.

” Zan koma inda na fi tasiri ne, inda nafi gogewa domin ci gaba da yi wa mutane na hidima da aiki.

” Ko a fadar shugaban kasa wasu da dama suna ta tambayata cewa me zai maida ni majalisa sai na ce musu ra’ayi na ne in koma majalisa.” Inji Yari

Idan har ya samu nasarar cin wannan zabe Yari zai wakilci Zamfara ta Yamma kenan a majalisar dattawan.

Share.

game da Author