Ina da tabbacin cewa Sule Lamido zai janye takarar sa don ni – Atiku Abubakar

0

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana wa dandazon magoya bayan sa a garin Dutse jihar Jigawa cewa yana da tabbacin Suke Lamido zai janye takarar sa domin shi Atikun.

” Sule Lamido kanina ne kuma ra’ayin mu daya a siyasa. Ina da tabbacin cewa zai janye mini takara domin in samu nasarar zama dan takarar shugaban cin Najeriya a PDP.

” Mahiafiyata yar asalin Dutse ce kafin suyi kaura zuwa yankin Adamawa.

Irin haka ne ya faru a wancan lokacin inda Umaru Musa ya hakura da takara domin wan sa Shehu Musa yayi takarar shugaban kasa. Duk anyi haka ne domin kada abin ya zama kamar na ‘yan gida daya ne.

Atiku ya garzaya jihar Jigawa ne domin neman amincewar wakilan PDP su mara masa baya domin samun nasarar zama dan takarar PDP a zabe mai zuwa.

Share.

game da Author