Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa ta na fatan batun zargin harkallar yin fojare na Satifiket din kammala bautar kasa da Kemi Adeosun ta tafka, zai kasance karya ce kawai.
Fadar ta yi wannan jawabi ne kwanaki 60 bayan da PREMIUM TIMES ta fallasa harkallar Kemi Adeosun, wadda ta mallaki katin shaidar kammala aikin bautar kasa na bogi, inda fadar ta ce ana ci gaba da bincike.
Sai dai kuma fadar ta kara da cewa gwamnati za ta dauki kwakwarar mataki da zarar an kammala bincike, an fitar da sakamako.
Tun bayan fallasa Kemi da kuma ganin an dauki lokaci gwamnati ba ta yi komai a kai ba, tuni wasu kungiyoyi suka rubuta wa Sugeto Janar na ‘yan sanda wasikar neman ya gaggauta binkiken Adeosun.
Haka ita ma wata kungiya mai suna SERAP ta maka hukumar NYSC kotu, saboda ta tsaya nuku-nukun bayyana ko Kemi ta mallaki takardar kammala NYSC.
“Batun nan dai zargi ne, kuma ana kan bincike. Da zarar an kamamala bincike kuma duk za a ga sakamako da matakin da za a dauka.
“Tun da magana na kan matakin bincike, ba zan yi gaggawar bayyana ranar da za a kammala ba.” Inji Garaba Shehu.
Idan ba a manta ministan harkokin kudi na Najeriya Kemi Adeosun ta buga satifiket din karya cewa an yafe mata yin bautar kasa NYSC a Najeriya bayan ta kammala Jami’a.
Wannan karya da ta lafta ya tada hankulan mutanen Najeriya matuka ganin cewa gwamnatin da take wa aiki gwamnati ce da ke bugun kirji da yin kururuwar ita gwamnati ce mai tsafta.
Tabbatattu kuma sahihan shaidun bayanai rubutattu sun tabbatar da cewa Ministar Harkokinn Kudi, Kemi Adeosun ba ta yi aikin bautar kasa ba, kuma a lokacin shekarun ta ba su kai na wadda aka dauke wa aikin bautar kasar ba.
PREMIUM TIMES ta gano cewa Kemi ta mallaki shaidar yin bautar kasa ne ta hanyar yin fojare, shekaru da yawa bayan da ta kammala jami’a.
Yan Najeriya sun harzuka sosai bayan fallasa harkallar da Ministar Harkokin Kudade, Kemi Adeosun ta yi, inda ya tabbatar da cewa kiri-kiri ta ki zuwa aikin bautarc kasa wato NYSC, a lokacin da ta kammala babbar kwalejin ta.
Akasarin wadanda suka tofa albarkacin bakin su, sun yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya kafa kwamitin bincike domin a tabbatar da gaskiya ko akasin gaskiyar wannan labara da PREMIUM TIMES ce ta bankado shi.
Mafi yawan wadanda suka yi rubuce-rubuce a soshiyal midiya, sun cika da mamakin yadda hukumomi da jami’an tsaron bincikenn kwakwaf suka kasa gano wannan bahallatsa ta Kemi, har sai da PREMIUM TIMES ta fallasa ta.
Takardun karatun Kemi da ke hannun PREMIUM TIMES sun nuna cewa an ba ta satifiket na yafe mata zuwa bautar kasa a shekarar 2009, a bisa yawan shekaru.
Amma sai dai ko uffan har yanzu gwamnatin Buhari bata ce ba game da haka.
Sai gashi kuma gwamnatin kiri-kiri ta daure wani ma’aikacin ta wai shima ya aikata irin haka.
Kotu ta daure wani ma’aikacin ma’aikatar Kudi ta tarayya mai suna James Lebi-Ayodele da ta kama da laifin buga satifiket din karya na kammala karatun samun kwarewa a harkar kudi.
Bayan haka James zai biya taran Naira 100,000.
Alkalin kotun Yusuf Halilu ya bayyana cewa yanke wa James irin wannan hukunci zai zama darasi ga duk masu buga satifiket din karya.
Sai dai kuma ita ministan kudi, Kemi Adeosun, da yake shafaffa da mai ce, sannan tana da uwa a gindin murhu, gwamnatin Najeriya ta kasa ce mata ko kala, duk da ta yi amfani da shaidar karya ta dare kujerun iko da dama a kasar nan kuma an samu tabbacin lallai satifiket din bogi ne ta yi ta amfani da har ta kai matsayin da take yanzu a kasar nan.