Masaniyar Ingancin abinci Grace Olasumbo ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji cin kayan itatuwan da aka nika su da sinadarin Calcium Carbide.
Olasumbo ta bayyana cewa Sindarin Calcium Carbide sinadari ne da mafi yawan ‘yan kasuwa ke amfani da shi wajen nika danyen kayan itatuwa, wato kayan marmari.
Bincike ya nuna cewa gajartan hakuri da hadama na cikin abubuwan da ke sa ‘yan kasuwa yin amfani da wannan sinadarin domin a cikin kwana daya yake nunar da kayan itatuwa.
” Shi wannan sinadarin kan nunar da kayan lambu ta yadda idan mutum ya gani zai yi sha’awar siya yayi amfani da shi.
Olasumbo ta bayyana cewa wani abin da ‘yan kasuwa suka kasa ganewa shine amfani da wannan sinadarin don nunar da kayan marmari na yi wa kiwon lafiyar mutane illa matuka
Cikin cututtukan da hakan ke kawowa ya hada da ciwon ciki, amai da gudawa, ciwon ido, gyanbon ciki,dajin makogwaro,baki,hanta da sauran su.
Olasumbo ta ce kayan marmarin da aka nika da wannan sinadarin a kasuwa na dauke da nau’in ruwan kwai sannan ba kowani bangare bane a jikinsu ke da wannan nau’in kuma yawancin su basu da dandanon da ya kamata.
Ta ce za a iya guje wa irin wadannan kayan ta hanyar siyan kayan marmari da aka tabbatar da ingancin nunan su
Bayan haka kakakin kungiyar masu siyar da lemu na jihar Kano Ado Shehu ya yi kira ga mutane musamman ‘yan kasuwa a kasar nan gaba daya da su ji tsoron Allah su guji amfani da wannan sinadarin wajen nunar da kayan marmarin su.
Shehu ya bayyana cewa tun da ma’aikatar kiwon lafiya ta wayar mu su da kai game da illolin da wannan sinadarin yake yi wa kiwon lafiyar mutane suka daina amfani da shi.
Discussion about this post