Hadarin jirgin kasa: Hadari ne ba Hari ba – Rundunar ‘Yan sanda

0

Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Kaduna Ahmad Abdulrahman ya karyata rade-radin da ake ta yadawa wai hadarin jirgin kasa da akayi jiya Lahadi a Kaduna, hari ne ba hadadri ba.

Idan ba a manta ba an sami rahotannin murkushe shanu 52 da jirgin kasa yayi a kauye kasarami, karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna.

Kwamishina Abdulrahaman da ya sanar da haka a Kaduna ya bayyana cewa hadarin ta auku ne da misalin karfe 11:45.

” Su dai wadannan makiyaya sun taso ne daga Kaduna zuwa Funtuwa sannan a dalilin rashin sanin ko jirgin kasa za ta yi aiki a wannan rana ne ya sa suka koro shanun su kan titin jirgin a daidai jirgi ya taso.

” Shanu 52 ne suka mutu, 27 suka sami rauni wadda kuma sarkin mahautan kauyen Kasaram ya yanka su nan take.

Babu ko mutum daya daya samu rauni a hadarin.

Abdulrahaman ya kuma karyata rade radin da wasu ke yi cewa wai ba jirgin kasa bane ya murkushe wadannan shanu ba, wai hari ne aka kawo.

” Wannan hadari ne ba hari ba. Sannan mun zauna da shugabanni da sarakunan wannan gari domin a samu zaman lafiya a tsakanin mutanen jihar.

Share.

game da Author