TATTAUNAWA: Yadda na boye daruruwan Kiristoci na hana a kashe su -Liman Abdullahi

0

Cikin wannan tattaunawa da Mataimakin Jakadan Amurka a Najeriya, David Young ya yi da Abdullahi Abubakar, Limamin nan da ya taimaka ya tsirar da wasu Kiristoci daga kisa a rikicin baya da aka yi a jihar Filato, limamin ya bayyaya dalla-dalla abin da ya faru.

TAM: Ko za ka fada mana kadan game da tarihin ka?

Abubakar: An haife ni a garin Akuyam, cikin jihar Bauchi. Na yi karatun Alkur’ani a garin Potiskum da kuma Gombe. Daga bisani kuma na dawo garin Gindin Akwati, cikin Karamar Hukumar Barkin Ladi ta jihar Filato, inda na ci gaba da zama tare da mahaifi na da wani dan uwa na.

A wancan lokacin na so na shiga aikin soja, domin a yi yakin Basasa da ni, amma sai mahaifi na ya ki amincewa, saboda a lokacin tsufa ya cim masa, kuma shi ne limanin garin, ni kadai ne zan iya taimakon sa. To da ya rasu sai aka nada ni limamin yankin, na gaje shi kenan.

Wato ba zan iya tuna rana ko shekarar da aka nada ni liman ba, amma ina ganin zai kai kamar shekaru 30 baya. Kun san abin an dade fa.

TAM: Shin me za ka iya tunawa ya faru a ranar 23 Ga Yuni, 2018 a cikin kauyen ku da ke karamar hukumar Barkin Ladi a jihar Filato ne?

Abubakar: Wato da misalin yamma, bayan Sallar La’asar, wadanda suka yi sallah ba su ma gama ficewa ba, sai muka fara jin harbin bindiga daga Gindin Akwati, inda ake harbin ba shi da wata tazara da kauyen mu.

Daga nan kuma sai muka ji harbin sai karuwa ya ke yi, domin daga kauyen Sai ma duk mu na jin harbi na tashi. Daga nan kuma sai kauyen mu ya rude, kowa na ta gudu daga maharan.

To da ya ke masallacin a bude ya ke, sai na rika kiran kowa ma ya zo ya boye a cikin masallacin gaba dayan Kiristoci da Musulmai. Ni da Na’ibi na muka rika cusa mutane a cikin gida na da cikin masallacin. Mu ka ce kowa ya kwanta a cikin masallacin don gudun kada harsashi ya samu wasu.

Daga nan sai muka kulle masallacin da kuma gida na mu ka tsaya waje don mu maida masu kai harin baya.

Muka rika rokon su da su wa Allah kada su kashe wadanda mu ka boye a cikin masallaci, da kuma cikin gida na.

A nan fa aka yi ta yin tataburza da su. Na dai cirje ina ba su hakuri kada su kashe Kiristocin da ke cikin masallacin ina ce musu sun rigaya sun zama baki na fa. To a wancan lokacin har maharan nan sun fara bazuwa su na zagaya ginin masallacin, da gida na, su na neman shiga. Na yi kokarin kiran waya, amma wayar ta ki shiga. Na kasa samun kowa.

TAM: Daga nan sai me ya faru da mutanen da ke boye a cikin masallaci da kuma gidan ka?

Abubakar: Cikin iko da kudirar Alah, haka dai muka yi ta rokon su kada su kashe mutanen nan da ke cikin gida na da cikin masallaci.

Ba za mu iya gane wadanda suka kai harin ba, saboda duk sun rufe fuskokin su. Mun dai yi ta rokon su mu na hada su da Allah, kada su kashe kowa.

Sai da ni na durkusa a gaban mutanen da ke dauke da bindigogi ina rokon su kada su kashe kowa. Can kuma sai na barke da kuka, ina wayyo, ina birgima a gaban su, kada su kashe kowa don Allah. Ina kuma cewa don Allah su tafi. Daga nan dai sai suka juya.

TAM: Yanzu ina mutanen da suka boye a cikin masallacin ka da kuma gidan ka suke?

Abubakar: Da suka gudo suka shige cikin masallaci da gida na, nan muka ci gaba da zama da su, bayan kai harin, muka ba su abinci kuma muka tsaya tare da su, har lokacin da aka zo aka kwashe su zuwa sansanin masu gudun hijira.

TAM: Fada mana dalilin da ya sa ka yi wannan kwakkwarar bajintar saida ran ceton wadaNnan dimbin jama’a haka?

Abubakar: Dalili na shi ne saboda tun da ni ke a kauyen nan, ina zaman lafiya da mutanen nan.

Ba mu taba samun wani sabani ko wata tankiya a tsakanin mu ba. Saboda zaman lafiya ma har auratayya ake yi a tsakanin mu. Ni kai na ina ma da jikoki wadanda ba musulmi ba, amma daga baya sun shiga musulunci.

Kuma bari ma na shaida maka wani muhimmin abu. Wadanda ba musulmi ba su ne da kan su suka ba mu filin da muka gina masallacin.

A lokacin bukukuwan sallah da kirsimeti kuma ana zaman lafiya. Mu kan kai wa juna ziyara kuma ana raba abinci ana aika wa juna.

TAM: Ya ka ji a jikin ka a ranar da abin ya faru?

Abubakar: Gaskiya abin ya tayar min da hankali, domin har na kai sati daya ban iya yin barci ba. Amma saboda karfin imani, sai na fawwala komai ga Allah, har ga shi a yanzu na fara wartsakewa.

TAM: Wane sako gare ka?

Abubakar: Kira na shi ne a zauna lafiya da juna. A guji kashe-kashe, domin Allah ne ya hada mu zaman tare a wuri daya.

Share.

game da Author