A makon da ya gabata labarai da dama sun dauki hankalin mutanen Najeriya inda aka yi ta yin muhawara da tattaunawa a shafunan sada zumunta na yanar gizo da shafin mu hausa.premiumtimesng.com kai tsaye.
1 – Gwamnatin Najeriya ta daure ma’aikacin ta a dalilin mallakar shaidar karya, amma ministar Kudi Kemi Adeosun na sheke ayar ta ba a iya ce mata uffan ba
Sai dai kuma ita ministan kudi, Kemi Adeosun, da yake shafaffa da mai ce, sannan tana da uwa a gindin murhu, gwamnatin Najeriya ta kasa ce mata ko kala, duk da ta yi amfani da shaidar karya ta dare kujerun iko da dama a kasar nan kuma an samu tabbacin lallai satifiket din bogi ne ta yi ta amfani da har ta kai matsayin da take yanzu a kasar nan.
Karanta nan: https://wp.me/s8iDgo-11857
2 – Halin da na samu Sambo Dasuki tsare a hannun DSS -Jones Abiri
ABIRI: Tabbas na hadu da Sambo Dasuki amma fa ba a daki daya aka tsare mu ni da shi ba. Kun san su ai manya ne. Amma fa duk da haka ina tabbatar muku da cewa a inda ya ke a tsare yanzu ko wurin bayan gida babu. A duk lokacin da ya matsu, sai dai su fito da shi su kai shi wani wuri can daban….,
Karanta nan: https://wp.me/p8iDgo-356
3 – Safiya Abubakar ta lashe gasar rubutun gajerun labarai ta BBC Hausa, ‘Hikaya’ ta 2018
Kamar yadda BBC Hausa ta wallafa a shafinta, alkalan Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta BBC Hausa, wato Hikayata, sun bayyana labarin ”Ya Mace’, a matsayin labarin da ya yi zarra cikin labarai sama da 300.
Karanta kalilan daga cikin labarain a nan: https://wp.me/p8iDgo-34G
4 – Za a fara yin fidar Zuciya a asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello
” Wannan shine karo na farko da asibiti a yankin Arewa zai fara yin irin wannan fida a Najeriya.
Wannan nasara da muka samu ya biyo bayan shekaru da dama da muka yi muna bincike da shiri domin haka.
Karanta nan: https://wp.me/p8iDgo-353
5 – Ku dawo gida daga kasashen da kuke, ana samun canji a Najeriya – Gwamnati
Gwamnatin Tarayya ta roki ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje da su dawo gida su taimaka a gina Najeriya, tare da sha musu alwashin cewa al’amurran Najeriya na samun canjin ci gaba sosai.
Karanta nan: https://wp.me/s8iDgo-11831
6 – Bayani kan cika sallah ga mai Kasaru, Tare da Imam Bello Mai-iyali
Ita Kasaru itace Sunnar matafiyi a cikin tafiyarsa, anfi son matafiyi yayi kasaru, don itace abinda Sunnah ta koyar, kuma tafi lada, ga sauki.
Karanta nan: https://wp.me/p8iDgo-34F
7 – Ina nan a kan baka ta na ‘giyar mulki na dibar Buhari’ – Atiku
” Buhari na tare da wadanda ke fada masa abin da yake so ya ji ne kawai. Idan ba haka ba ta yaya za a ce gwamnatin da ta cire tallafin rarar mai, sannan ta kara kudin mai, amma ace wai kuma ta fi gwamnatocin baya biyan kudin tallafin rarar mai .
Karanta nan: https://wp.me/s8iDgo-11816
8 – Mata ta kashe kanta a dalilin kama mijinta da wata a gadon su na aure
Wata matar aure mai suna Kafilat ta kwankwadi ruwan guba a dalilin kama mijinta Ismail da ta yi da wata a kan gadon su na aure.
Karanta nan: https://wp.me/s8iDgo-11814
9 – Tuba nake Sarki, Guiwowi na a kasa – Zango ga Ali Nuhu
Adam Zango ya roki Ali Nuhu da ya yafe masa laifukan da yayi masa, yana mai cewa “Tuba nake Sarki, Guiwowi na a kasa” kamar yadda ya rubuta a shafin sa ta Instagram.
Karanta nan: https://wp.me/p8iDgo-34s
10 – Kungiya ta siya wa Buhari fom din takara
Kungiyar NCAN ta mika wa shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole chekin miliyan 45 da ta biya a banki don siyan fom din.
Karanta nan: https://wp.me/p8iDgo-344
Karanta sauran a nan: hausa.premiumtimesng.com
Discussion about this post