Fadar Shugaban Kasa ta karyata zargin da aka yi cewa Shugaban Ma’aikatan fadar na da hannu a wata harkallar karbar cin hanci har ta Naira miliyan 29.
Kakakin Fadar Shugaban Kasa Garba Shehu ne ya maida wannan kakkausan martani, musamman bayan da jaridar Punch ta buga labarin.
Wani mutum ne da ya yi ikirarin cewa shi dan’uwan Abba Kyarin ne, a kwanan nan ya shiga wata kafar yada labarai ya ce ya ba shi cin hancin naira miliyan 29.
Rahoton ya ce Abba Kyari ya rika yin amfani da mutumin wajen tafka harkallar cin hanci sau da yawa.
A kan wannan ne a cikin wani jawabi da Garba Shehu ya fitar, ya yi tir da rahoton da Punch ta buga inda mutumin ya yi zargin cewa Abba Kyari ya karbar masa naira miliyan 29 da nufin za a ba shi kwangila.
Shehu ya ce zargin duk kirkirar karya ne kawai, domin Kyari bai ma taba ganawa da murtumin su biyu ba.
Shehu ya kara cika da mamakin cewa bai san dalilin da ya sa Punch ta buga labari irin wannan da bai da tushe ko kamshin gaskiya ba, alhali kuma tuni Hukumar Tantance Kwangiloli ta bayyana cewa wanda ya yi zargin ba ma’aikacin ta ba ne.
Daga nan kuma Sai ya yi nuni da cewa wasu ‘yan siyasa ne ke hada baki da wasu kakafen yada labarai saboda ganin zabe ya matso, suke sa wa Buhari matsin-lamba ta hanyar kirkiro harkallar da ba ta faru ba, ana jinginawa ga gwamnatin sa.
Bugu da kari, Shehu ya karyata batun kwangilar sayo motoci samfurin Hilux guda 15 da aka yi magana, domin a ta bakin kakakin na Buhari, babu ma wannan zancen a cikin kasafin 2016 da na 2017.
“Binciken da muka yi ya tabbatar da cewa kasafin 2016 da 2017 sam babu batun sayen motoci kirar Hilux 15. Don me za a ce Abba Kyari ya nemi a ba shi cin hanci a kwangilar da babu ita a cikin kasafin kudi?
Fadar Shugaban Kasa ta ci gaba da nuni da cewa Abba Kyari ya fi karfin ya nemi cin hancin naira miliyan 29, domin kuwa an yi shirin biyan ofishin sa har naira miliyan 200 duk wata amma ya ki amincewa cewa ba ya so sai naira miliyan 29 zai karba don cin hanci.
” Tun a lokacin da jaridar Punch ta ke neman bayanai kan wannan labari mun sanar musu cewa babu gaskiya a hujjojin da sukr dogaro da amma suka yi mana kunnen uwar shegu suka wallafa wannan labara ba tare da tantance hujjojin su ba.
” Yanzu dai ga fili-ga-doki, sai suyi shirin fafatawa da Abba Kyari a Kotu.” Inji fadar Shugaban Kasa.