Shehu Sani ya sayi fom din takarar sanata na Kaduna ta tsakiya

0

Sanatan dake wakiltar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani ya sayi fom din takarar kujerar Sanata ta Kaduna ta Tsakiya.

Yanzu dai karara hakan na nuna cewa za a gwabza ne tsakanin sanata Shehu Sani ne dake kan kujerar da Uba Sani, wadda shine mai ba gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufai shawara kan harkokin siyasa a zaben fidda gwani.

Idan ba a manta ba Sanata Shehu Sani da wasu gungun ‘yan jam’iyyar APC daga jihar Kaduna sun nuna adawar su ga amincewar jam’iyyar a jiha na yin zaben fidda dan takara ta hanyar yin amfani da zababbun wakilan jam’iyya wato ‘Indirect’ maimakon ‘direct’ wato ‘kato na bin kato’ da su suke so.

Daruruwan magoya bayan sanata Shehu Sani ne suka yi takkaki daga Kaduna zuwa Abuja domin raka sanata Shehu Sani siyan fom din sake takarar kujeran Sanata.

A jawabin da yayi wa mutane a ofishin jam’iyyar APC, Sanata Sani ya godewa mutanen jihar musamman na shiyyar Kaduna ta tsakiya da suka biyo shi har Abuja domin yi masa rakiya.

Ya ce suna nan kan bakan su na a yi zaben fidda dan takara ta hanyar amfani da salon ‘kato a bayan kato’ wato Direct maimakon wanda jam’iyyar a jiha ta amince da shi.

Share.

game da Author