Shugaban Kwamitin Dattawan Jam’iyyar PDP, Walid Jibrin ya bayyana wa manema labarai cewa jam’iyyar na kokarin ganin ta rage yawan ‘yan takarar shugaban kasa da suka bayyana ra’ayin su.
‘Yan takara 13 ne zuwa yanzu suka bayyana ra’ayin su na bugawa a zaben fidda dan takara.
Walid ya ce kwamitin sa na kokarin ganin ta zauna da ‘yan takaran domin a samu daidaituwa a tsakinin su domin a rage yawan su daga 13.
Bayan haka yayi kira ga sauran mambobin kwamitin na dattawar jam’iyyar da su nisanta kansu da ga nuna inda ra’ayin su ya karkata.
Ya ce a matsayin su na dattawa bai kamata ace wani ya karkata ga dan takara ba.
Shi ko tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido a lokacin da yake mika fom din sa na takara ya gargadi jam’iyyar ne da kada su tsoma bakin su kan abin da ya shafi dan takara.
Ya ce dan takara na jama’an Najeriya ne ba na jam’iyya ba. Sune suke da iko kan wanda za su zaba.
A karshe yayi kira ga jam’iyyar da ta tabbata an tsayar wa ‘yan Najeriya dan takara da suke so da kuma zai yi tsairi a zaben 2019.
Discussion about this post