Ina nan a kan baka ta na ‘giyar mulki na dibar Buhari’ – Atiku

0

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa yana nan a kan bakan sa cewa giyar mulki diban shugaban Kasa Muhammadu.

Atiku ya zayyano wasu dalilai da ya ce gazawa ne na gwamnatin APC da kuma nuna iko da karfin mulki da take amfani da su wajen yin abin da ta ga dama a kasara nan.

” Idan ba mulkin kama karya ba, kiri-kiri ministan shari’a ya tafi kotu ya karbo iko daga kotu da aka dakatar da majalisar dattijai binciken wanda ya saka hannu aka dawo da Abdulrashid Maina kasar nan.

” Buhari na tare da wadanda ke fada masa abin da yake so ya ji ne kawai. Idan ba haka ba ta yaya za a ce gwamnatin da ta cire tallafin rarar mai, sannan ta kara kudin mai, amma ace wai kuma ta fi gwamnatocin baya biyan kudin tallafin rarar mai .

” Ba zai yiwu ace an kara kudin mai da kashi 68 bisa 100 ba sannan kuma ace wai ana biyan kudin rarar mai fiye da yadda gwamnatin Jonathan ta biya ba duk da ana saida mai a Naira 87 lita daya awancan lokacin, yanzu kuwa ana saida wa naira 145.

” Bayan haka idan aka duba za a ga cewa maimakon mu sauko daga tsanin cin hanci da rasahawa da muke can sama a da kara lulawa muka yi duk da kururuwar da gwamnatin Buhari keyi na wai tana yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan.

“Ina kira ga Buhari da makarraban sa da su koma su sake yin nazarin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Idan ba a manta ba fadar Shugaban Kasa ta maida martani ga Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, wanda ya ce giyar mulki na diban Buhari sannan ba ya saurara wa kowa kafa.

Atiku ya ce ya fara nuna damuwa dangane da shin ko zaben 2019 zai yiwu ko ba zai yiwu a bisa adalci da gaskiya in dai Buhari na kan mulki ba.

A cikin wata hira da ya yi da AFP, tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce ba kamar Goodluck Jonathan ba, wanda ya mika mulki a ruwan sanyi, bayan zaben 2015. Yanzu kasar nan inji Atiku ta fada hannun wani tsohon soja kuma wanda giyar mulki ta diba wanda ba zai yarda mulki ya subuce daga hannun sa, a cikin ruwan sanyi sai an fafata da shi.”

“Sai dai kuma a cikin martanin da aka maida wa Atiku, a yau Laraba, fadar sa ta amince da cewa Buhari ya cika zare wa jama’a jan-idanu amma fa wajen hana su sata da wawuke kudin gwamnati, fadar ba ta yarda da cewa Buhari ya bari giyan mulki ta dibe shi ba.

“ Giyan mulki bata dibi Buhari ba. Sannan musamman Shugaba Buhari yayi ayyukan raya kasa a dukkan fadin kasar nan wadanda zai iya bugun kirji da su har ma ta fito sake tsayawa takarar shugaban kasa.”

Share.

game da Author