KANJAMAU: Wayar wa mutane kai shine mafita – Aisha Buhari

0

Uwar gidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta yi kira ga kungiyoyi da su kara maida hankali wajen yawaita tunatar da mutane game da cutar Kanjamau.

Aisha ta yi wannan kira ne a taron tsara hanyoin wayar matasa game da cutar kanjamau a kasashen yankin Afrika da Sin da uwargidan shugaban kasar Sin, Peng Liyuan ta shirya.

Ta ce yin haka ya zama dole ganin cewa matasa sun fi fadawa hadarin kamuwa da yada cutar.

Peng Liyuan ta jinjina wa kokarin da kasashen yankin Afrika suka yi wajen ganin mutanen dake dauke da cutar sun sami magani da kare yara kanana daga kamuwa da cutar.

Share.

game da Author