Ba mu amince da zaben fidda dan takara na amfani da ‘Wakilai ba – Shehu Sani

0

Sanatan dake wakiltar Kaduna ta tsakiya Sanata Shehu Sani da wasu gungun ‘yan takara sun yi wa uwar jam’iyyar APC wasikar nuna kin amincewar su da shirin gudanar da zaben fidda ‘yan takara na jam’iyyar APC ta hanyar amfani da wakilai.

A wasikar da suka rubuta wa shugaban jam’iyyar Adams Oshiomhole, ‘yan takaran sun bayyana cewa wannan shiri ne da wasu kalilan za su yi amfani da karfi su nada wadanda ba sune ra’ayin jama’a ba.

” Dukkan mu da muka saka hannu a wannan takarda na adawa da shirin yin zaben fidda ‘yan takara a jihar Kaduna ta hanyar ‘Wakilai’ wato ‘indirect’ maimakon ta hanyar kai tsaye.

” Wannan tsari na zaben fidda dan takara ta hanyar yin amfani da wakilai tsari ce da ba zai yi tasiri a jihar ba. Tsari ce ta kama karya.

Yan takaran da suka sa hannu a wannan takarda sun hada da

Shehu Sani- senator Kaduna central senatorial district

Mohammed Sani- senatorial aspirant Kaduna central senatorial district

Aliyu Silver- senatorial aspirant Kaduna North senatorial district

Shamsuddeen Shehu- senatorial aspirant Kaduna central

Rufai chanchangu- member representing Kaduna South federal constituency

Mohammed Musa-member representing Soba federal constituency

Halal falal- gubernatorial aspirant

Usman Ibrahim- senatorial aspirant Kaduna central district

Hassan Samdi- aspirant Kaduna North federal constituency

Umar Isa- aspirant Kaduna South federal constituency

Aminu Sa’ad – aspirant Kaduna South federal constituency

Yusuf Ali- aspirant Kaduna South federal constituency

Sani Nagari -aspirant Chikun/Kajuru federal constituency

Rufai Surajo- aspirant Kaduna North federal constituency

Sani Abdul -Doka/ Gabasawa constituency.

Share.

game da Author