Osinbajo bai amince da ra’ayin Buhari kan ‘Yan sandan jihohi ba

0

Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya fito karara ya nuna rashin amincewa da Shugaba Muhammadu Buhari dangane da batun damka wa jihohi ikon kafa ‘yan sanda a jihohin su.

Osinbajo ya ce shi dama ya dade ya na da wannan ra’ayi na a kafa ‘yan sandan jihohi, kuma ya dade ya na neman a kafa su din.

Ya ce tsarin aikin ‘yan sanda a karkashin gwamnatin tarayya ba shi da ingancin wanzar da ayyukan tsaron da ake so su rika yi.

“Na sha cewa a kafa ‘yan sandan jihohi, saboda aikin tsaron al’umma aiki ne na kusanci da al’umma, saboda haka ba fa za ka iya kula da tsaron al’ummar kasar nan idan ka na zaune daga Abuja ba.”

Hakan kuwa ya nuna Osinbajo ya nesanta kan sa daga ra’ayin Shugaba Buhari, wanda tuni ya yi watsi da batu da kuma bukatu da koke-koken a kafa ‘yan sandan jihohi a kasar nan.

Buhari ya tsaya a kan cewa babu isassun kudade da kuma tattalin arziki mai karfin da zai iya daukar dawainiyar biyan albashi da kuma tafiyar da ayyukan ’yan sandan jihohi a kasar nan.

Wani karin dalili da Buhari ya tsaya a kai dai shi ne akasarin jihohin idan aka bar su, ba za su iya daukar nauyin biyan albashin ‘yan sandan da za sun dauka ba.

Yawancin jihohi dai duk cima-zaune ne, ba su iya daukar nauyin kan su da kan su, sai sun jira tallafi a kowane wata daga gwamnatin tarayya.

“Shin jiha nawa ce ke iya daukar nauyin kan ta da kan ta? Ai ba za ka cika bindiga da albarusai ba sannan ka ba mutum, ka ce ya yi maka aiki, alhalin ba ka iya biyan sa. Kai ma ka san abin da zai kasance daga nan kuma.” Haka Buhari ya bayyana a wata hira da yayin da Sashen Hausa na Muryar Amurka cikin watan Mayu.

Share.

game da Author