Buhari ya fadi dalilin sa na kin sa wa Kudirin Zabe hannu

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya ki sa hannu a kan Kudirin Gyaran Dokar Zabe na 2018, wanda ya bayar da dalilin wasu “hardaddun batutuwa” da ba a warware ba a lokacin da aka aika aiko da kudirin daga Majalisa.

Mai Taimakawa Na Musamman a Harkokin Majalisar Dattawa, Ita Enag ne ya bayyana haka a cikin wani jawabi da ya fitar a Abuja.

Ya ce tuni shugaban kasa ya sanar da majalisar dattawa da ta tarayya hakan tun a ranar 30 Ga Agusta.

Shugaban Kasa, ya ki sa hannu ne kan Kudirin Gyaran Dokar Zabe, saboda har yanzu akwai sauran rina a kaba, domin akwai sauran batutuwan da majalisa ba ta tabo ba a lokacin da ka gabatar da kudirin.

“Shugaban Kasa ya gayyaci Majalisar Dattawa da Ta Tarayya domin su zauna a warware zare da abawar da suka hargitsa daurin dokar zaben da hanzari, domin shi ma ya gaggauta sa wa dokar hannu.”

Ya ce akwai batu na abinda Doka ta Sashe na 87 (14) na dokar zabe ya tanada, wanda ya yi magana kan takamaimen ranakun da za a gudanar da zabukan fidda-gwani na jam’iyyun siyasa.

“Domin hakan ya na iya kawo cikas ta INEC, yadda zai rage saura kwanaki tara kawai ya rage wa hukumar zaben ta kammala jerin sunayen ‘yan takara da na jam’iyyun siyasa da kuma dawainiyar gudanar da zaben fidda gwanin jam’iyyun siyasa har 91.”

Ya ce Majalisar ta yi gaggawar aika wa Shugaban Kasa Kudirin Dokar Gyaran Ranakun Zabe, ba tare da yin la’akari da yinn gyara a sashen doka na 31, 34 da kuma na 85 ba.

Share.

game da Author