Tsohon gwamnan jihar Kano, kuma dan takarar shugaban Kasa a inuwar jam’iyyar PDP Ibrahim Shekarau ya fice daga jam’iyyar.
Yau Sule, kakakin Shekarau ya bayyana wa BBC Hausa cewa Shekarau ya fice daga APC ne a dalilin rashin adalci da aka nuna masa a PDP tun bayan dawowar Kwankwaso.
Sule ya ce iwar jam’iyyar ta rusa zababbun shugabannin jam’iyyar na jihar Kano babu gaira babu dalili.
” Wadannan shugabannin jam’iyya suna zangon su ta biyu ne amma maimakon a bari su kammala wa’adin su sai aka rusa su.
” Sannan kuma cikin shugabanni 7 shida daga cikin su duk an ware wa mutanen Kwankwaso ne.
” Wannan rashin adalci da aka yi mana bai dace ba. A jihar Sokoto gwamnan jigar Tambuwal ya sauya sheka zuwa PDP amma ba a canza tsarin jam’iyyar ba, me ya sa sai a jihar Kano.
Shekarau dai bai bayyana ko wacce jam’iyyar zai koma ba tukunna.
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne Ibrahim Shekarau, ya tabbatar da cewa yawar ‘yan takarar da ke nuna tsayawa a zaben 2019 a karkashin PDP, ba zai haifar da rudani a cikin jam’’iyyar ba.
Ya fadi haka ne a garin Bayelsa, a ziyara da ya kai wa gwamnan jihar, Seriake Dickson.