An kama miyagu sama da 1000 dake ke hana mutane sakat a titin Abuja – Kaduna cikin shekara daya – Moshood

0

Kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya Moshood Jimoh ya bayyana wa taron manema labarai cewa jami’an rundunar ‘Kakkabe miyagu, da tabbatar da zaman lafiya’ sun kakkabo miyagu sama da dubu zuwa yanzu a titin Abuja-Kaduna.

Moshood ya kwarmata wa ‘yan jarida haka ne a garin Tafa, dake karamar Hukumar Kagarko, jihar Kaduna da ya ke fadin nasarar da jami’an tsaro suka samu na kama wasu ‘yan ta’adda 32 a wannan titi.

Yace wadannan kame-kame da ake yi ya zarce har yankin Zamfara, Kogi, Plateau, Sokoto da FCT.

Ya kara da cewa an kwato bindigogi kirar AK 47 22 da albarusai, da mota kirar Toyota.

Cikin wadanda aka kama, akwai barayin shanu, Masu garkuwa da mutane ‘yan fashi da sauran muggan mutane.

Bayan haka ya karyata rade-radin da ke ta yadawa wai duk an saki wadanda jami’an tsaro suka kama tun da ka fara farautar wadannan ‘yan ta’adda, cewa ba a saki ko da mutum daya ba.

” Babu wanda muka saki, duk wanda aka kama za a gurfanar da shi gaban kuliya, inda za a yanke masa hukunci bisa ga abin da ya aikata.”

Share.

game da Author