Kungiyar EU za ta tallafa wa kasashen da ke kewaye da tafkin Chadi

0

Kungiyar hadin kan kasashen turai EU ta bayyana cewa za ta tallafa wa kasashen da ke kewaye da tafkin Chadi da kudade har yuro miliyan 232.

Jami’in kungiyar Christos Stylainides ya sanar da haka a taron da aka yi a Berlin kasar Jamus.

Ya ce EU ta bada wadannan kudade ne domin tallafawa mutanen da hare-haren Boko haram ya yi wa illa da wadanda canjin yanayi ya shafa a yankin kasashen da ke kewaye da tafkin Chadin.

Ya ce kasashen da EU za ta tallafa wa sun hada da Najeriya, Kamaru, Nijar da Chadi.

” A fannin inganta halin rayuwa za mu ba wa Najeriya Yuro miliyan 47 million, Nijar €15, Chad €11.8 da Cameroon €15.1 sannan a fannin samar da ci gaba Najeriya za ta sami Yuro miliyan 74.5, Nijar €32.2, Chad €33.2 sannan kasar Kamaru miliyan €2.7.

Bayan haka jami’ar EU Neven Mimica ta bayyana cewa wannan tallafi zai karkata ne wajen bunkasa fannin kiwon lafiya, ilimi, tattalin arziki, da sauran su.

A karshe ta kara da cewa tallafa wa wadannan kasashen ya zama dole musamman ganin cewa akalla mutane miliyan 2.4 suka rasa matsuguni a yankin sannan mutane miliyan 3.6 na fama da matsinacin yunwa wasu miliyan 17 sun talauce a dalilin Boko Haram da canjin yanayi.

Share.

game da Author