Shugaban kwamitin riko na karamar hukumar Charanchi dake jihar Katsina Yusuf Radda ya bayyana cewa akalla mutane 15 sun rasu a sandiyyar kamuwa da cutar Amai da Gudawa.
Radda ya ce karamar hukumar ta gaggauta samar da magungunan cutar sannan mutane 24 da suka kamu da cutar na samun kula a asibitin dake Charanchi.
Sannan ya na rokon gwamnatin jihar da ta kawo musu dauki domin su sami nasara a aikin da suka sa a gaba na kau da cutar kwata-kwata a karamar hukumar.
Discussion about this post