Gwamnatin Najeriya ta dauki tsauraran matakai don ganin ana amfani da katin nan mai launin rawaya da ake kira ‘Yellow Card’ da ke nuna shaidar yin rigakafin zazzabin Shawara ga musamman masu tafiye-tafiye kasashen waje.
Jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar kiwon lafiya Olajide Oshundun ya bayyana haka inda ya kara da cewa gwanati ta yi haka ne ganin cewa an yi fama da cutar a kasar nan a wannan shekara.
Ya ce kafin a samu wannan kati sai mutum ya biya kudi a banki sannan ya kawo shaidar biyan wannan kudin daga bankin zuwa ma’aikatar kiwon lafiya sannan bayan ya yi allurar sai ya karbi katin.
Sai dai wani gudu ba hanzari ba PREMIUM TIMES ta gano cewa mutane da dama idan za su yi tafiya su bar kasa kan sami wannan kati ba tare da sun yi allurar rigakafin cutar shawara ba.
Wakiliyar mu ta gana da wata mata mai suna Rahanat inda ta yi mata bayanin cewa ta sami wannan kati ba tare da ta yi allurar ba a kan Naira 2,500.
‘‘Tun da aka fada mun cewa bazan iya tafiya ba tare da wannan kati ba na fara neman samun wannan kati a nan tashar jiragen saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
‘‘Da na je sai na yi wa matar dake zaune a wurin karyan cewa ina tsoron karban allura daga nan ta ce na biya Naira 2,500 ta bani katin.
Shima wani Tony mai shekaru 40 ya ce tabbatar cewa ya karbi wannan kati ba tare da yin allurar ba a kan Naira 3000.
Wani jami’in ma’aikatar kiwon lafiya ya karyata wannan magana cewa wai ana smun katin ba tare da anyi wa mutum rigakafin ba.
” Ina tabbatar muku cewa ma’aikatar mu ba za ta bada katin nan ba ba tare da yi wa mutum rigakafin ba.
Shima jami’in hukumar hana yaduwar cututtuka Ayoola Olufemi ya bayyana cewa samun katin na da matukar mahimmanci.
” Tun da cutar shawara ta bullo a shekarar bara gwamnati ta fara yi wa mutane rigakafin cutar.