Yadda Saraki ya shirya wancakalar da Buhari a 2019

0

Mawallafin Mujallar Ovation, Dele Momodou, ya bayyana cewa a wata sabuwar hira da yayi da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, gogan ya zayyano wasu hanyoyi da dabarun yadda zai doke Buhari a zaben 2019.

Dele ya fadi cewa sun yi wannan hira ne da Saraki ya bayyana masa wadannan hanyoyi a garin Ilori a ziyarar barka da sallah da ya kai masa.

Sarki ya ce ” Gaba daya lissafin Buhari bai wuce yadda alkiblar siyayar bangarancin sa yake ba cewa idan dai mutum ba daga yankin Arewa Maso Yamma ya fito ba bazai ci zaben Najeriya ba.

” Tun da dama can inda akalar tasu ya karkata zuwa kenan, cewa idan dai ba daga yankin Arewa Maso Yamma ko Arewa Maso kudu dan takarar shugaban kasa ya fito ba babu wanda zai iya gwara wa da Buhari, abin da za kayi shine ka dinke yankin Arewa Maso Tsakiya Tamau, ka rabu da su su yi ta Arewa Maso Yamman su.

” Ya ce bata lokacin ka za ka yi ka nemi kuri’u daga yankin da Buhari ke da karfi. Kai dai ka nemi samun kashi 25 bisa 100 na kuri’un da za akada a wadannan yankuna kawai.

” Idan PDP suka fidda dan takarar da bashi da farinjini toh ko Buhari da yangar sa zai gangara fadar gwamnati a karo na biyu Sannan kuma mutane da dama ba za su yi zabe ba.

” Da aka tambaye shi game da ko a wani bangaren kasar nan zai dauko mataimakin sa sai yace a yankin Kudu maso Kudu ko Kudu masu Gabas ne zai dauko mataimakin sa domin ay wai Kudu maso Yamma sun sami nasu.

Bayan haka yayi kira ga Buhari ya ya mika kan sa domin ayi mukabala dashi kowa ya san abinda aka yi na ainihi da wadanda ba a yi ba.

Share.

game da Author