2019: ‘Kabali da Ba’adin’ da ta dabaibaye ’yan takarar shugaban kasa a PDP

0

Idan ba taka-tsantsan aka yi ba, jam’iyyar PDP za ta iya tsintar kan ta a cikin wata gagarimar rafkannuwar da idan ba ta yi aune ba, to ‘kabali ko ‘ba’adin’ siyasa ba zai iya gyara rikirkicewar ta ba, ballanta har ta yi tunanin sake komawa kan mulki a zaben 2019.

PDP DAGA JIYA ZUWA YAU

Tun bayan da aka hambarar da jam’iyyar a kan kujerar mulki a zaben 2015, bayan shafe shekaru 16 da ta yi daure da zaren damben dukan jam’iyyun adawa, a yanzu kuma jam’iyyar ta yi ta kokarin yi wa kan ta wanka da sabulu tare da fesa turare, har ta fara jawo sabbin mambobi, da nufin sake kwace mulki daga hannun APC a zaben 2019.

Sai dai kuma wannan muradi na ta zai iya samun babbar barazana, ganin yadda ‘yan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar sun fi dozin daya, kuma kowanen su ya na harin shi ya ke so PDP ta tsaida takara a zaben shugaban kasa na ranar 16 Ga Fabrairu, 2019.

JERIN CARBIN ‘YAN TAKARAR SHUGABAN KASA: Wane ne ba wane ne ba?

Ya zuwa yanzu akwai gagga kuma mashahuran ‘yan takara har 14 da ke ta kai gwauro sun a kuma kai mari domin ganin kowa shi aka tsaida a takarar shugaban kasa a gangamin da jam’iyyar za ta yi, cikin watan Oktoba, watanni biyu kafin karshen shekara.

Yayin da suka fara banke-banken juna wajen yankan fam na neman tsayawa takara, har ma wasu sun fara kaddamar da gangamin fitowar su takara, wasun su sun fara fitowa su na cewa ko da sun fadi ko an kayar da su a zaben fidda-gwani, to ba za su fice daga jam’iyyaaarrr ba.

Haka Rabi’u Kwankwaso, Ahmed Makarfi, Atiku da Sule Lamido suka bayyana kwanan nan.

‘Yan takarar sun hada da Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso, Sule Lamido, Ibrahim Shekarau, Ahmed Makarfi da kuma Attahiru Bafarawa.

Akwai kuma Ibrahim Dankwambo, David Jang, Tanimu Turaki, Datti Baba-Ahmed da kuma na kwana-kwanan nan, irin su Aminu Waziri Tambuwal da Bukola Saraki, wanda a ranar Alhamis da ta gabata ya ayyana kudirin sa na neman fitowa takara.

Dukkan wadannan ‘yan takara dai duk daga Arewa suke, alamar da ke nuna cewa daga Arewa dan takarar PDP zai fito kamar yadda na APC shi ma din daga Arewa zai fito, wannan bai hana wasu daga Kudu yin katsagallin neman fitowa takarar shugaban kasa a karkashin PDP ba.

Gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose mai barin gado da tsohon gwamnan jihar Cross Rivers, Donald Duke, duk sun fito sun muna muradin su.

A shekaru 20 da aka shafe bayan rada wa jam’iyyar PDP suna, ba a taba samun rubdugun ‘yan takarar shugabancin kasa ba kamar a wannan zabe mai zuwa na 2019.

Tun a zaben 1999 da ‘yan takara irin su Olusegun Obasanjo, Alex Ekweme, Phillip Asiodu, Don Etiebet, Graham Douglas, Jim Nwobodo da kuma irin su Fransis Ellah, Richard Akinjide, Abubakar Rimi, Adisa Akinloye suka nemi takara.

Sai dai kuma Obasanjo ne ya yi nasara, a taron gangamin da PDP ta gudanar a garin Jos, babban birnin jihar Filato.

KAKAGIDAN ‘YAN AREWA A TAKARAR PDP: Kowa ta sa ta fisshe shi

Kwamitin da jam’iyyar PDP ta kafa bayan shan kaye a zaben 2015, wanda Ike Ekweremadu ya shugabanta, ya sahale cewa a zaben 2019, daga Arewa dan takarar jam’iyyar PDP zai fito, tunda Goodluck Jonathan da aka kayar shi kua daga kudu ya fito.

To amma kuma kusan tsikar jikin kowane dan PDP a tashe ta ke, ganin shin a cikin wadannan dandazon ‘yan takara, wane ne a za iya daura wa banten kokawa har ya kayar da abokin kafsawa na jam’iyyar APC, wanda ko shakka babu, Shugaba Muhammadu Buhari ne za su tsaida?

Abin tutiya dai kusan dukkan ‘yan takarar su na da tagomashi da kuma kumbar susar da za su iya yakushin APC a kumatu har su yi mata lahani.

Majiya mai tushe dai ta nuna tabbas babu wanda zai iya janye wa wai a takarar, har sai an je fitin zaben fidda-gwani tukunna, kowa ya nemi sa’a.

A gefe daya dai tabbas alamomi sun tabbatar da cewa duk wanda aka kayar a zaben fidda-gwani, ba zai fusata ya canja jam’iyya, wato ya fice daga PDP ba.

Sai ma tayar da kayar baya da wasun su ke ta yi su na zagayen neman jama’a a fadin jihohin kasar nan 36. Sannan kuma su na kara neman goyon baya daga sauran jam’iyyu 36 da suka hade wuri guda a karkashin Hadaddiyar Rudunar Jam’iyyun Siyasa, (CUPP).

Kwakkwarar majiya daga cikin PDP ta tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa jam’iyar na murna da yawan ‘yan takarar, domin ko ba komai za ta kara samun kudin shiga ta hanyar sayen fam. Sai dai kuma babbar damuwar ita ce wanda za ta iya tsaidawa ba tare da kaurewar sabani ko babbar rajin jituwa ya farraka jam’iyyar bayan ta tsaida dan takarar ta ba.

Ana ta rade-radin cewa dukkan ‘yan takarar za su rattaba hannun amincewa sakamakon zaben fidda-gwani, tare da alkawarin cewa duk wanda ya fadi ba zai fice daga PDP a fusace ba. Sannan kuma su yarda za su taya shi kamfen ka’in da na’in.

KARBA-KARBA A CIKIN KARBA-KARBA?

Da ya ke tsarin karba-karbar da PDP ta amince da shi, ya nuna daga Arewa dan takarar shugaban kasa zai fito, sai daya daga cikin ‘yan takarar, Sanata Rabiu Kwankwaso ya ce idan ana so a guji shigar sabani, to bayar da takarar ga Yankin Arewa maso Yamma.

Wannan shiyya ta kunshi jihohin Kano, Katsina, Kaduna, Kebbi, Jigawa, Sokoto da Zamfara.

Abin nufi, daga nan kuma sai wata shiyyar ta karba ita ma.

Yankin Arewa maso Yamma dai shi ne ya fi yawan al’umma a Arewa.

Idan aka dubi yawan ‘yan takarar, za a ga cewa akasarin su daga Arewa maso Yamma din suke.

Baya ga Kwankwaso, sauran irin su Lamido, Shekarau, Bafarawa, Turaki, Datti-Ahmed and Tambuwal duk daga wannan yanki suke.

Daga Atiku Abubakar, Saraki, Jang da kuma Dankwambo ne daga wasu shiyyoyin kadai a Arewa.

Idan har jam’iyyar PDP ta yi amfani da shawarar Kwankwaso, to ‘yan takara bakwai ne kadai za su gwabza a zaben fidda gwani kenan.

TSORON BAI WA YANKIN AREWA MASO YAMMA TAKARA

Na farko dai PDP na tsoron cewa idan ta takaita takara a cikin ‘yan yankin Arewa maso yamma kadai, ana tsoron wasu ‘yan yankin su yi tawaye, su ce an yi musu rashin adalci, ba a bar dimokradiyya ta yi aikin ta ba.

Na biyu kuma akwai tsoron idan APC ta tsaida Buhari, kamar yadda shi za ta tsaida, to kuri’in yankin za su kasu ne, APC ita ma za ta yagi rabo mai yawa kenan.

Musamman kwamitin kamfen din Atiku ya yi wannan korafin a baya, cewa idan aka ce Arewa maso Yamma kadai za ta fitar da dan takara, to an tauye wa sauran yankin ‘yancin su na zaben dan takara ko fitowa kenan.

Share.

game da Author