Najeriya zata ciwo bashin dala miliyan 382 daga Chana

0

Najeriya ta bada sanarwar za ta ciwo bashin zunzurutun kudi har dala miliyan 328 daga Chana domin inganda haryar fasahar sadarwar zamani, wato ICT.

Hakan ya na daya daga cikin yarjeniyoyin da za a kulla a tsakanin kasashen biyu, yayin wannan taro na Hadin Guiwar Inganta Tattalin Arziki da zai gudana a kasar tsakanin 3 zuwa 4 Ga Satumba, 2018.

Shugaba Muhammadu Buhari tuni ya isa kasar Chana tare da tawagar ‘yan rakiya masu tarin yawa, domin kai ziyara ta kwanaki shida, kuma an yi masa kyakkyawar tarba.

A lokacin rattaba hannu kan wannan yarjejeniyar ciwo bashin, Buhari zai zauna zaman kwarya-kwaryan bikin sa-hannun karbar lamunin tare da takwaran sa na China, Xi Jinping.

Yarjejeniyar dai za a kulla ta ne karkashin Hukumar Kula da Inganta Sadarwa da Fasahar Zamani ta Kasa, a tsakanin Galaxy Backbone Limited da kuma Huawei Technologies Limited (HUAWEI) a kan tsabar kudi har dala milyan 328.

Yarjejeniyar dai ta nuna cewa Exim Bank na kasar Chana ne zai samar da kudaden.

Najeriya za ta yi amfani da tsarin lamunin ne domin inganta fasahar sadarwa a karkashin shirin NICTB 11, wanda ke cike da muradin wannan gwamnati na inganta tattalinn arziki a tsarin fasahar sadarwar zamani, ICT domin samun nasar Shirin Farfado da Tattalin Arzikin Najeriya, ERGP.

Akwai kuma wasu karin yarjeniyoin da za a sa hannun amincewa tsakanin Najeriya da China a wannan ziyara. Haka ma sauran kasashen Afrika da ke hakartar taron za su yi na su yarjeniyoyin daban.

A bangaren Najeriya dai akwai yarjejeniya da Hukumar Inganta Zuba Jari ta Najeriya, Hukumar Kula daAlbarkatun Man Fetur ta Kasa sai kuma wasu yarjeniyoyi da kungiyoyin ‘yan kasuwa, masana’antu, albarkatun kasa da kuma ayyukan noma, wato NACCIMA.

A wannan sanarwa da kakakin yada labaran Shugaba Buhari, Garba Shehu ya bayar, ya ce ciwo bashin zai kasa samar da inganta tattain arziki tare da samar da ayyukan yi ta hanyar inganta sadarwar fasahar zamani a Najeriya, wanda ya ce ke samun koma baya da kuma kalubale ga kasa wajen tafiyarwa da kuma gudanar da tsare-tsaren ci gaba a Najeriya.

Share.

game da Author