Shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa na jihar Neja Garba Salisu ya bayyana cewa zuwa yanzu mutane 14 ne aka tabbatar an rasa a sanadiyyar ambaliya da akayi ta fama da shi a wasu kananan hukumomin jihar.
Salisu ya ce hukumar ta dauki masu ninkaya 200 aiki domin taimaka wa ayyukan hukumar musamman wajen ceto mutane.
Daga nan sai ya yi kira ga mutanen jihar da su gujewa yin gine-ginen gidajen su a hanyoyin ruwa.
” Mutane sukan gina gidaje a hanyoyin ruwa da hakan ke sa da zaran an yi ruwa mai yawa sai ya bi ta hanyoyin da aka gina wadannan gidaje.
” A wasu lokuttan akan yi ruwa da daddare ne da hakan ke sa kafin mutane su ankara an rasa rayuka. ” Inji Salisu.