Wani matashi mazaunin garin lafiya jihar Nasarawa ya bayyana cewa yakan yi cinikin akalla Naira 6,000 duk rana a yi wa mutane cajin waya.
Matashin mai suna Ibrahim Usman ya bayyana cewa da wannan sana’a ne ya ke ciyar da iyalan sa da kuma yin wasu hidimomin sa.
” A dalilin rashin wutan lantarki da ake fama dashi a garin Lafiya, a kullum sai nayi cinikin akalla Naira 6000.
” Rashin wutan lantarki a koda yaushe ne babban dalilin da ya sa muke samun ciniki.
Usman ya ce tan fatan a samu wuta a ko-ina a jihar da kasa baki daya.
Discussion about this post