Zazzabin Lassa ya bullo a jihar Enugu

0

Babban sakatare a ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Enugu Ifeanyi Agujiobi ya bayyana cewa zazzabin Lassa ya bullo a jihar.

Ya fadi haka ne wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, sannan ya kara da cewa cutar ta yi ajalin mutum daya a asibitin dake garin Enugu.

” An sami tabbacin cewa wannan mutum na dauke da zazzabin Lassa bayan gwajin da aka yi masa sannan duk da maida hankali da aka yi a kan sa, ya rasu.

Agujiobi ya ce ma’aikatar su ta fara gudanar da bincike domin gano tushen bullowar cutar.

” Za kuma mu gwada duk ma’aikatan kiwon lafiya da suka kula da wannan mutum a lokacin da yake jinya, mu kuma hada da ‘yan uwan sa da sauran mutanen da ya yi hulda da su domin dakile duk wata hanya da cutar za ta yadu.”

A karshe Agujiobi ya ce za su fara wayar wa mutane kai game da cutar da hanyoyin guje wa kamuwa da cutar a harshen Igbo a gidajen radiyoyin jihar.

Share.

game da Author