ZARGIN ZAMBA: An damke wani sojan Amurka a Najeriya

0

‘Yan sandan Hana Fashi da Makami, F-SARS, sun bayyana cewa sun damke wani sojan Amurka da ke zargi da yin 419 a Jihar Imo.

Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Dasuki Galadanchi, ya ce an kama Garrick Micheal da sauran wadanda ake zargi da aikata wasu laifuka da suka hada da fashi da makami, satar mutane tare da yin garkuwa da su da kuma safarar kananan yara.

Dukkan masu aikata wadannan mabambantan laifuka dai an fito da su an gabatar da su a gaban manema labarai a hedikwatar ‘yan sanda da ke Owerri.

Dasuki ya ce Micheal dan asalin kasar Amurka ne wanda ya kware sosai wajen zambatar mata makudan kudade da karyar cewar zai shirya musu biza zuwa Amurka.

Ya bayyana cewa ya zambaci Sylva, Chineyenwa, Wuchi Peace da kuma Duny Glory.

Micheal ya ce ya dawo Najeriya domin ziyartar matar sa ne daga nan kuma ya hadu da wanda ya zambata din.

Sai dai kuma ya ce harkar mu’amalar da ya yi da matar ba zamba ba ce, kasuwanci ne.

Share.

game da Author