Za mu rufe yin rijistar katin zabe daga ranar 17 ga watan Agusta – INEC

0

Hukumar (INEC) ta sanar cewa baza ta wuce ranar da ta tsayar domin rufe yin rajistar masu neman katin zabe ba.

INEC ta tsayar da ranar 17 ga watan Agusta a matsayin ranar da za ta rufe yin rijistan katin zabe domin samun damar buga wa wadanda tayi wa rijista katin zaben da kammala sauran shirue-shiryen da ya kamata ta yi kafin lokacin zaben 2019.

Jami’in hukumar Mohorret Bigun ya sanar da haka da yake ganawa da wakilan Kamfanin dillancin Labaran Najeriya ranar Laraba a Gombe.

Bigun ya ce hukumar za ta kara ranakun aiyukkan ta domin mutanen da basu sami yin rajista ba su samu yi.

” Daga ranar daya ga watan Agusta za mu fara aiki daga ranar Litini zuwa Lahadi daga karfe tara na safe zuwa biyar na yamma, amma kuma daga ranar 17 ga watan Agusta za mu ruge yin rijista sai kuma Allah ya kaimu bayan zaben 2019.”

A karshe Bigun ya yi kira ga mutanen da basu da katin zabe da su yi kokarin yin rijista kafin ranar 17 ga watan Agusta.

Share.

game da Author