Cibiyar Tabbatar da Ingancin Dimokradiyya, CCD, ta shirya gudanar da gagarimin taro a Najeriya domin tattauna hanyoyin da za a shawo kan yada labarai na kirkirar karairayi a na watsawa shafunan yanar gizo.
Za a gudanar da wannan taro ne domin magance wannan matsala kasancewa ga zaben 2019 ya kusanto, wanda dama saboda zaben ne aka shirya gudanar da taron.
Taron mai take: “Dimokradiyya da Labarai Na karya: Yadda Labaran Bogi ke wa ‘Yancinmu da Dimokradiyya Barazana”, za a kwashe kwanaki biyu ana gudanar da shi, a tsakanin 7 da kuma 8 Ga Agusta, a Abuja.
Daraktan CCD, Idaya Hayat ya bayyana cewa shirya taron a wannan lokacin ya yi daidai ganin cewa ya zo daidai da lokacin da zaben 2019 ke kara gabataowa, kuma ana ta kara samun yawaitar kafafen yada labarai na jabu.
“A halin yanzu filin dagar yakin neman zabe na ‘yan siyasa ya dau harami, har ya fara zafi, tun ma lokacin fara yakin neman zaben bai zo ba tukunna. Ga shi ana fama da matsalar tsaro da matsalar tattalin arziki. Don haka ana fargabar kada ‘yan siyasa su yi amfani da wannan dama wajen yada ji-ta-jita ko kuma tauye ma’aunin labarai domin karkatar da masu kada kuri’a daga zaben wadanda ra’ayin su ya fi karkata a kai.”