‘Yan majalisa shida sun koma PDP daga APC a jihar Kano

0

‘Yan majalisar dokokin jihar Kano su shida sun fice daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar PDP a yau Laraba.

Wadannan ‘yan majalisa sun sanar da ficewar su ne a wata wasika da suka mika a zauren majalisar.

A wasikar da kakakin majalisar Kabiru Rurum ya karanta ‘yan majalisar sun bayyana ficewar su bisa ga dalilan gazawa wajen cika alkawarun da suka dauka wa mutanen a karkashin jam’iyyar APC.

Wadanda suka canza shekan sun hada da Yusuf Babangida Sulaiman (Gwale), Rabiu Saleh (Gwarzo) , Zubairu Mahmud (Madobi), Yusuf Abdullahi Falgore (Rogo), Hamza Sule (Bichi) da Isiaku Ali Danja (Gezawa).

Idan ba a manta ba a dalilin ajiye aiki da mataimakin gwamnan jihar Kano Hafiz Bello ya yi, wasu daga cikin hadiman gwamna da da suke tare da Hafiz sun mika takardar ajiye aikin su.

Wadanda suka ajiye aikin sun hada da Bakari Ado, Habibu Abubakar, Idris Rogo, Rukayya Jibrin
Hafiz Bichi, Alhaji Nagoda, Shamsu Kura, Kasim Jingau, Kasim Bichi.

A ranar Lahadin da ya gabata ne mataimakin gwamnan jihar Kano Hafiz Bello ya mika takardar ajiye aiki wato sauka daga kujerar mataimakin gwamnan jihar Kano.

Kakakin Hafiz, Abdulwahab Ahmad ne ya mika wa PREMIUM TIMES kwafin takardar.

A cikin takardar, Hafiz ya bayyana cewa sam baya jin dadin yadda suke aiki da gwamnan jihar Abdullahi Ganduje.

” Kwata-kwata gwamna Ganduje ba ya daraja kujera ta na mataimakin sa. Ko na bada shawara ba ya dauka da hakan yasa muka fada cikin kamayamayar da jam’iyyar ta shiga a yanzu a jihar.

” Na yi ta fama da bakin ciki, zaman maraici da kakanikayi duk a dalilin rashin daraja ni da kujerar da nike zaune a kai. A haka ne na yi shawara sannnan na yanke hukuncin hakura da aikin kawai.

Shi dai Hafiz Abubakar makusancin sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da ake ganin nan ba da dadewa ba zai canza sheka ya koma PDP.

Share.

game da Author